Mai dokar barci: Yansanda sun kama wani Sojan Najeriya yana tafka abin kunya a Gombe
Yansandan Najeriya sun kama Soja da wasu mutane 19 sakamakon aikata muggan laifuka
Rundunar Yansandan jahar Gombe ta sanar da kama cafke wani jami’in rundunar Sojan kasa na Najeriya dake aiki da runduna ta 301 a garin Gombe da aikata laifin fashi da makami tare da wasu mutane goma sha tara, inji rahoton kamfanin dillancin labaru NAN.
kwamishinan Yansandan jahar Gombe, Muhammad Mukaddas ne ya bayyana a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba yayin da yake ganawa da yan jaridu a babban ofishin Yansandan jahar.
A cewar Kwamishina Muhammad Mukaddas, jami’in Sojan ya hau babur ne a ranar Laraba daga babban titin garin Gombe zuwa kauyen Tabra, amma yayin da suka raba hanya, sai nuna dan achaban bindiga ya kwace masa babur.
“Yansandan jahar Gombe sun kama wani jami’in Soja mai suna Ojobo Sunday, karamin Soja dake aiki da runduna ta 301 dake garin Gombe da laifin aikata fashi da makami. Sojan ya dauki dan achaba mai suna Abubakar Garba akan ya kaishi kauyen Tarba daga babban titi.
“Amma yayin da suke kan hanya sai ya nemi dan achaban ya tsaya akan cewa yana bukatar kiran waya, tsayawar dan achaban keda wuya sai ya nuna masa bindiga kirar AK 47, sa’annan ya kwace babur din kirar Bajaj ya tsere.
“Sai dai tashinsa keda wuya sai dan achaban ya buga ihu yana kiran jama’a su taimakeshi, daga nan ne waasu yansanda dake sintiri a mota suka cimmasa, inda suka kamashi. Tuni ya amsa laifinsa, kuma zamu gurfanar da shi gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike.” Inji kwamishina.
A wani labarin kuma, kwamishinan Yansandan ya bayyana cewa sun kama mutane goma sha tara da laifuka daban daban da suka danganci fashi da makami, satan babur, sayan kayan sata da kuma laifin kisan kai.
Haka zalika yace sun kama wata mata da ta jefar da dan jaririnta mai kwanaki biyar a duniya, inda yace dukkanin mutane goma sha taran zasu fuskanci sharia da zarar an kammala bincikensu.
Friday, 30 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: