Thursday, 29 November 2018

Tsintuwa ba sata ba: Wani dan baiwa ya tsinci Naira biliyan 2 cikin wata dilar gwanjo

Tsintuwa ba sata ba: Wani dan baiwa ya tsinci Naira biliyan 2 cikin wata dilar gwanjo

Hausawa dai na cewa tsintuwa ba sata ba, idan mai abu ya gani a bashi abun shi. Haka nan wasu kuma na cewa idan Allah ya soka da arziki to tsintuwa yake sawa kayi kamar daga sama.

To wannan ma dai labarin kusan a iya cewa haka ne domin kuwa wani ne Allah yayi wa gam-da-katar bayan da ya tsinci dame a kala lokacin da ya siya wata taskira ta adana muhimman abubuwa akan Naira 182,000 amma sai ya tsinci Naira biliyan 2.

wani sanannen mai gabatar da shire-shire a wani gidan Talabijin din kasar Birtaniya da kuma yake sayar da gwanjo, Dan Dotson ne ya bayar da wannan labarin a cikin shirin nasa da yake gabatarwa.

Sai dai da fadin hakan, sai kau akayi sa'a wadanda suka sayar da ma'ajiyar tun asali suka ji labari inda suma suka tada balli kan cewa lallai-lallai sai dai a tada ciniki ko kuma dan basu wani kaso a cikin kudin.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: