Tuesday, 27 November 2018

GYARAN KIRJIN KI ( NONO )


Kowanne miji akwai irin abinda yafi burgeshi a jikin matar Sa. yi kokarin Ki dinga sarrafa masa wannan abinda zai ja hankalin Sa.

Ki zama mai biya masa bukatarsa dabarun bayyanar
 da tudun kirjinki ga mijinki. Idan kinki to akwai Mata masu tallar Abubuwan ar'ha zai gani office ko kasuwa da bakin titi.Da zarar kin Fara haihuwa musamman kirjinki bai da tudu to Ki daina zama ba rigar mama.
Tsabtace rigunan mamanki akai-akai da fesa musu turare masu kamshi. Daga rigunan mamanki sun Fara saki , yi maza Ki sake sababbi.

Ki dinga siyan ( 12 ) ko ( 6 ) kadai ma zasu isheki.
Sai sunfi dadewa basu Saki ba, idan rigar mama ta saki nono baya tsayawa cak. Ba'a Sa turare a nono, maigidanki na Sa baki zaiji daci. Barin maigidanki yayi wasa dasu, kuma da tsotsarsu na sawa su ciko.
Ki kiyaye magungunan na bature da wadanda basu da inganci. Kirjinki dukiyarkice kar garin gyara gira a rasa Ido.

Ki godewa Allah a yarda ya halicceki duk yadda kike akwai wacce bata Kai kiba. Halittarki da kiketa korafi, wata kuma shi take kwadayin samu.

Ki nemi hanyoyin na halal don inganta kirjinki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: