Tuesday, 27 November 2018

Yayinda ake kai ruwa rana kan mafi karancin kudi N30,000 a Najeriya, kasar Afrika ta kudu ta kara nata zuwa N126,480




Kasar Afrika ta kudu ta kara kudin albashin ma’aikata mafi karanci zuwa N126,480 a wata, Wannan labara na zuwa ne yayinda ake cigaba da kai ruwa rana kan mafi karancin albashi a Najeriya N30,000.

Shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana cewa za’a fara biyan wannan sabon albashi daga ranan 1 ga watan Junairu, 2019, kuma ma’aikata miliyan shida ne zasu amfana.

Gabanin wannan kari, ma’aikatan kasar South Africa sun kasance suna karban N97,49 matsayin kudi mafi karanci.

Kudin South Africa Rand 1 daidai ne da N26.35 a kudin Najeriya. Wannan na nuna cewa ma’aikatan kasar Afrika zasu dinga karabn N4,216 a kowace rana sabanin yan Najeriya da har yanzu babu tabbacin zasu samu N1000 a rana.

Kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa N30,000 yayi yawa kuma ba zasu iya biya ba. Amma idan aka tilastasu su biya, sai dais u kori ma’aikata.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Ayuba Wabba, ya bayyana cewa kungiyar zata zauna ba dadewa ba domin baiwa gwamnati daman karshe da zata game shawararta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: