Ko kunsan irin sirrikan da cin ayaba kedauke dashi musamnan ga da namiji?
Akwai nau'ikan abinci da dama dake kara lafiya da kuzari a jikin mutane. Ayaba na daga cikin 'ya'yan itace dake taimakawa halittun jikin mutum, musamman wajen tasirinta ga kuzarin 'ya'ya maza.
Bincike ya tabbatar da cewar cin ayaba guda daya a kowacce rana zai matukar inganta lafiyar 'ya'ya maza ta hanyoyi da dama,
Bayan kasancewar ta abinci maras maiko, ayaba na taimakon aiyukan halittun jikin mutum da su ka hada da; cire kitse maras amfani daga jikin mutum, tana inganta aikin kwakwalwa ta hanyar kara ma ta karfi, sannan tana saka jiki samar da sindarin "serotonin" da ke saka walwala da annashuwa.
A cikin ayaba akwai sinadarai da dama da suka hada da; vitamin A, B, E da PP, sinadarin kalshiyum, ayon, sodiyom, maganeziyum, da fasfaros. Wadannan sinadarai na da matukar tasiri wajen inganta aikin kwakwalwa da halittun jima'i.
Sirrikan cin ayaba ga namiji
Amfanin ayaba bai kare iya nan ba, binciken masana ya tabbatar da cewar yawan cin ayaba na hana jini ya hau sannan tana maganin matsalolin uwar hanji.
Sai dai masana sun ce akwai wasu yanayi da idan mutum ya samu kansa a ciki, to ya kauracewa cin ayaba, yanayin su ne; idan jinin mutum na samun matsalar yawan daskarewa, idan mutum na da matsalar toshewar jijiyoyin jini a cikin zuciya, da ma su fama da cutar da sukari.
Duk da amfanin da ayaba ke da shi, masana sun ce a kula da adadin da za a ke ci a kowacce rana.
0 comments: