Monday, 26 November 2018

Subahanallahi! Ankama Malamin Islamiyya ya yi wa wata yarinya 'fyade' a Kano





Rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano ta kama wani malamin,Islamiyya mai shekaru 41, bisa zargin bata wata yarinya 'yar shekara takwas.

Yarinyar dai na daya daga cikin wasu yara bakwai da aka dauke shi musamman don ya rika koyar da su ilimin addini gidansu.
Mai magana da yawun reshen rundunar ta jihar Kano, Sufuritenda Magaji Musa, Majiya ya shaida wa AbdusSalam Ibrahim Ahmed, cewa sun sami kwararan hujjojin gurfanar da malamin a gaban kuliya, kuma iyayen yarinyar sun yi tsayuwar daka a kan a bi masu hakki.

Ya ce malamin ya yi amfani da wasu dubaru na janyo hankalin yarinyar har ya yi lalata da ita a bayan gidansu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: