Monday, 24 December 2018

ASUU zatai watsi da Gwamnati inji Shugaban Kungiyar



Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya watau ASUU ta bayyana cewa babu mamaki ta daina kula gwamnatin kasar. Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana mana wannan a Ranar Lahadin nan a cikin Garin Legas.

Farfesa Biodun Ogunyemi, ya zanta da manema labarai inda yayi jawabi game da kokarin da su ke yi na ganin an gyara harkar ilmi a kasar nan. Ogunyemi yace sun aika takardu kuma sun gana da gwamnati amma abubuwa sam sun ki gyaruwa.

Kungiyar ta ASUU tace da alama ba za ta sake halartar wani zama da gwamnati ba, har sai ta nuna da gaske ta ke yi wajen cika alkawarun da ta dauka a baya. Ogunyemi ya zargi Jami’an gwamnati da kin fadawa Duniya gaskiyar abin da ke wakana.

Shugaban na ASUU yace gwamnatin tarayya ba ta da niyyar shawo karshen wannan yajin aiki da ake yi illa iyaka ta rabu da Malaman makarantar su na surutu.

Farfesa Biodun Ogunyemi yace sun yi zama har 6 mma har yanzu babu alamun nasara.
Biodun Ogunyemi yake cewa gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka da kan ta a 2009 da kuma 2017. Farfesan yace gwamnati ba ta sakin kudi domin inganta harkar ilmi yadda ya kamata kuma ba ta yarda da kwamitin Wale Babalakin ba.

Malaman Jami’an dai sun dauki watanni kusan 2 su na yajin aiki, inda su kace babu abin da ya hada yajin aikin na su da zaben 2019. Shugaan kungiyar yace babban burin su shi ne a inganta harkar ilmi a Najeriya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: