Buhari ya sha tafi da ihu a Majalisa
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha ihu a majalisar dokoki yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019,
Shugaban ya sha tafi daga magoya bayansa amma 'yan adawa sai ihu suke suna cewa 'karya ne' yayin da yake jawabi kan nasarorin gwamnatinsa a majalisar da jam'iyyar PDP ke jagoranta,
Shugaban ya isa majalisar tare da ministocinsa kuma an yi tafi na cewa 'sai baba' da kuma sowa lokacin isowarsa.
Shugaban dai na gabatar da jawabi gaban 'yan majalisar wakilai da 'yan majalisar dattawan kasar ne da kuma ministocinsa da gwamnoni,
Sai dai wasu 'yan majalisar na yi masa ihun rashin amincewa da bayanin ayyukan da ya ce gwamnatinsa ta yi a fadin kasar.
Wasu 'yan majalisar kuwa suna yi masa tafi tare da furta kalaman karfafa masa guiwa.
0 comments: