Sunday, 16 December 2018

Muhammad Salah shine dan wasan kwallon kafa daya doke Okocha a tarihin kollon Africa




Muhammad Salah shine dan wasan kwallon kafa daya samu nasara a wannan shekara, ya samu masoya sama da 650,000 da suka zabe shia Dan wasan yaci kwallo 44 a cikin wasanni 52.
Moh Salah, dan Kwallon kasar MAsar, ya doke Okocha a tarihi a Afirka

Egypt da Liverpool sun bayyana cewa an zabi Muhammad Salah a matsayin wanda aka zaba a dan wasan dayafi kowa.
Shine dan wasan daya kere wa sa'a a wannan lokaci run bayan Bolton da Najeriya a tsakanin Jay Jay da Okocha a shekara ta 2003 da 2004.

Sama da masoya 650,000 ne suka zabi dan wasan mai shekaru 26 Muhammad Salah, inda ya doke Medhi Benatia,Kalidou Koulibaly,Sadio Mane da kuma Thomas Partey inda ya karbi lambar girmamawa.


Dan wasan na Premier League a wannan shekara ya ciyo kwallo 44 daga cikin wasanni 52 da aka buga.
Salah ya bayyana tsantsar farin cikin sa bisa ga wannan nasara daya samu inda yake cewa

"Nayi matukar murna da wannan nasara sannan ina fatan wata shekarar na kara samun nasara"

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: