Monday, 10 December 2018

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace Alhaji Dan Musa Ribah, jigo a jam'iyyar PDP a jihar Kebbi,



An sace dan siyasar ne a garin Ri
bah da ke karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar.
Majiyar mu ta shaida mana cewar dan siyasar bai dade da canja sheka daga APC zuwa PDP ba, kuma an sace shi ne da misalin karfe 3:00 na daren ranar Lahadi. Wasu 'yan bindiga ne cikin kayan jami'an 'yan sanda suka sace shi, kamar yadda iyalinsa suka fada,

Garin Ribah na kan iyakar jihar Kebbi da Zamfara, mai fama da hare-haren 'yan bindiga.

Wani daga cikin iyalan dan siyasar ya ce; " wasu 'yan bindiga ne da kayan 'yan sanda suka zo gidanmu da misalin karfe 3:00 na dare kuma suka tafi da shi,

'Yan bindiga sun sace jigo a PDP daga arewa
"Har yanzu bamu san inda yake ba. A gaban matansa da 'ya'ya suka tafi da shi zuwa wurin da har yanzu babu wanda ya sani.

"Muna rokon jami'an tsaro da su taimaka su gudanar da bincike a kan lamarin domin har yanzu mutanen garin Ribah na zaune cikin tashin hankali ."

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kebbi, DSP Danjuma Possi, ya tabbatar da cewar an sanar da su batub sace dan siyasar. Kazalika ya yi alkawarin tuntubar manema labarai da zarar an samu wani sabon labari.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: