Monday, 10 December 2018

Wannan wanne irin Rashin imani ne? Uwargida ta kashe kanta da yayanta biyu saboda Magida zai ƙaro amarya




Ke duniya ina zaki damu ne, har yanzu kuma da alama har gobe dadaddiyar dabi’ar nan ta mata watau kishi ba zai taba rabuwa dasu ba, tunda dai ta tabbata har a zamanin iyaye da kakanni ma an yi kishi da juna, sai dai kishi na irin wannan zamani na neman ya wuce gona da iri.

Anan mun samu rahoto wata Mata yar kasar Kenya mai suna Ruka Wasuna mai shekaru 26 da ta halaka kanta, sa’annan kafin nan ta halaka yayanta data haifa guda biyu kawai don mijinta ya kamma shirin dauko mata abokiyar zama, watau amarya, ko ace kishiya.

matar nan ta kashe kanta da yaran nata ne ta hanyar banka ma gidansu wuta dake unguwar Otongole a yankin Kisumu, wanda ya konasu kurmus, ba don komai ba sai don bacin ran data shiga a sakamakon kishin daya turnuketa saboda mijinta uban yayanta zai kara aure,

Mai unguwan Otongole, Simon Osege Orwa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun kaddamar da bincike a matakinsu, sa’annan ya kara da cewa matar ta dauki wannan mummunan mataki ne saboda rashin jituwa da ta samu da mijinta,

Mai unguwa Osege ya bayyana cewa mijin matar na shirin kara aure ne ba tare da sanin matarsa Rukia ba, amma ranar da ta samu labarin, sai ta garzaya wani gidan mai dake makwabtaka dasu, ta sayo fetir galan daya wanda tayi amfani dashi wajen banka ma gidansu wuta.

Daga karshe Mai Unguwa Osege ya bayyana cewa mijin matar na bakin aikinsa a kamfanin Eldoret ne a lokacin daya samu labarin abinda ya faru, amma tuni Yansanda sun isa idan lamarin ya faru suka kwashe gawarwakin mamatan.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: