Friday, 7 December 2018

Wasu na Neman Hanyar da zasu samu, wasukuma nakin abun. Tsageru sun hana Jami’an Gwamnati raba tallafin TRADERMONI

Tsageru sun hana Jami’an Gwamnati raba tallafin TRADERMONI

Wadannan Matasa sun hana a bada gudumuwa a kasuwar Ilorin
Jama’a sun ci buri za su samu wannan kudi amma aka tada rikici

Rikici ya sa an gaza rabawa 'Yan kasuwa kudin TraderMoni a kasuwar Ilorin
Mun samu labari daga Hukumar NAN mai dillacin labarai a Najeriya cewa wasu tsageru sun kawo hatsaniya a cikin Garin Ilorin a Jihar Kwara a daidai lokacin da Jami’an Gwamnati ke shirin raba tallafin nan na TraderMoni jiya da safe,

Wadannan fitinannun mutane sun hargitsa kasuwar Garin Ilorin a sa’ilin da ake kokarin bada gudumuwa ga masu karamin karfi a cikin kasuwar. Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan Matasa su na sanye ne rigunan Atiku,

An ce wadannan Matasa sun iso kasuwar ne dauke da hotunan ‘Dan takarar PDP na Shugaban kasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP inda su ka hana Ma’aikatan Gwamnati raba kudin da aka soma badawa ga kananan ‘yan kasuwa,

Wadannan Bayin Allah sun bada korafin cewa Mahaifin Shugaban Majalisar Dattawa, Olusola Saraki, shi ne wanda ya bada filin da aka gina wannan kasuwa a Garin don haka Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba za su yi wannan aiki a kasuwar ba.

Jami’an BOI na Gwamnatin Tarayya sun yi kokarin bada N10, 000 ne ga masu kananan kasuwanci a cikin Jihar Kwara kamar yadda aka soma tuni, amma abin ya gagara,  Hakan ta sa dai dole aka kira Jami’an tsaro domin gudun wata fitina.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: