Babbar Magana: Wani saurayi ya kashe budurwarsa tare da binne gawarta a dakinsa
Wani saurayi da aka bayyana sunansa da Prince Owabie, ya kashe budurwarsa wacce kuma ke dauke da cikinsa, tare da binne gawarta a cikin dakinsa a garin Fatakwal
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 2 ga watan Disamba, a sha-tale-talen Wimpy, titin Ikweere
- Rundunar 'yan sanda ta ce wanda ake zargin an kaishi zuwa sashin bincike masu aikata laifukan ta'addanci na jihar
Saurayi da aka bayyana sunansa da Prince Owabie, ya kashe budurwarsa wacce kuma ke dauke da cikinsa, tare da binne gawarta a cikin dakinsa a garin Fatakwal.
Owabie, wanda aka fi sani da J-BOY ya tonawa kansa asiri, bayan sanar da abokansa kwanaki biyu da wannan aika aikar da yayi.
Sai dai, cikin rashin sa'a ga J-BOY, abokan nasa suka sanarwa rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers wacce kuma ta tura jami'anta suka cafko shi.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 2 ga watan Disamba, a sha-tale-talen Wimpy, titin Ikweere,
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Nnamdi Omoni, ya ce wanda ake zargin an kaishi zuwa sashin bincike masu aikata laifukan ta'addanci na jihar.
DSP Nnamdi ya kara da cewa rundunar ta tura jami'anta zuwa wurin da lamarin ya faru don tono gawar.
"Muna da kwararan bayanai kan cewar J-BOY ya haka rami a cikin dakinsa inda ya bunne budurwarsa," a cewarsa.
0 comments: