Tuesday, 22 January 2019

Babbar magana: Yan sanda sun harbe mutane 3 a wani bata kashi da akai a jahar Rivers

Babbar magana: Yan sanda sun harbe mutane 3 a wani bata kashi da akai a jahar Rivers


Rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers ta ce ta samu nasarar harbe wasu da ake zargin 'yan bindiga ne guda uku har lahira
Rundunar ta ce 'yan bindigar da ta harben. ana zarginsu da kashe wani Mr Nnafor Ogbu, shugaban kungiyar matasa ta Ogale Eleme da ke jihar

Omoni mai magana da yawun rundunar ya ce rundunar ta kwato bindigar maharba guda daya da kuma gidan harsasai guda 11 a hannun 'yan ta'addan

Rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers ta ce ta samu nasarar harbe wasu da ake zargin 'yan bindiga ne guda uku har lahira, bayan da aka yi zargin sun kashe wani Mr Nnafor Ogbu, shugaban kungiyar matasa ta Ogale Eleme da ke jihar.

Mr Nnamdi Omoni, mai magana da yawun rundunar, kuma mataimakin sufurtandan 'yan sanda (DSP) ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Fatakwal a ranar litinin cewa 'yan ta'addar sun kutsa kai gidan Ogbu da ke Ogale. karamar hukumar Eleme inda suka harbe shi har lahira.

A cewarsa, Mr Elijah Eleke, DPO na yankin, ya gaggauta daukar jami'an rundunar zuwa farautar 'yan ta'addan, Omoni ya ce rundunar ta ci karo da 'yan bindigar ne a sha tale-talen matatar man fetur ta Fatakwal.

A cewarsa, ba tare da bata lokaci ba, 'yan ta'addar suka budewa jami'an rundunar wuta. Inda suma jami'an suka mayar da martani, wanda ya jawo musayar wuta tare da nasarar kashe 'yan ta'adda guda ukku, yayin da sauran suka tsere,
Ya kara da cewa an kai gwarwakin zuwa dakin ajiye gawarwaki.

Omoni ya ce rundunar ta kwato bindigar maharba guda daya da kuma gidan harsasai guda 11 a hannun 'yan ta'addan.
Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni rundunar ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin tuhumarsu da kuma gurfanar da su gaban shari'a domin yanke masu hukunci.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: