Thursday, 17 January 2019

Hukumar INEC ta saki jerin 'yan takara na zaben dazai gabata a kakar shekarar 2019

Channels TV da kuma shafin jaridar The Punch, mun samu cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta saki jeranto na karshe mai manuniya ga sunayen 'yan takara da za su fafata a babban zabe na bana.


jeranton ya kunshi sunayen 'yan takarar kujerar shugaban kasa, Sanatoci, 'yan majalisar wakilaii ta tarayya da kuma 'yan majalisar dokoki na jihohin kasar nan.

Babbar hukumar zabe ta kasa wato INEC, Independent National Electoral

Commission, ta bayar da shaidar wannan rahoto cikin wata sanarwa da ta wassafa a shafin zauren sada zumunta na Twitter mai lakabin @inecnigeria.


Jeranto na 'yan takarar kujerar shugaban kasa ya kunshi jerin sunaye 144 da kuma jam'iyyun su da ya hadar da sunayen 'yan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa


Jam'iyyar SDP.
Social Democratic Party, ta gaza gabatar da dan takarar ta na kujerar shugaban kasa da kuma mataimaki a sakamakon dambarwa ta rikicin siyasa da ke tsakanin tsohon ministan labarai, Jerry Gana da kuma tsohon gwamnan jihar Cross River, Mista Donald Duke.

Tsaffin kusoshin gwamnatin biyu na ci gaba da gajon hakuri na tsayar da dan takara guda a tsakaninsu, inda tuni kotu ta gyagije wajen lankaya takarar a hannun tsohon Ministan na Labarai.

A wani bangaren kuma, tsohon gwamnan na Cross River ya yiwa umarnin kotun kunnen uwar shegu, inda jam'iyyar ta SDP a karan kanta ta ci gaba da rikon sa a matsayin dan takarar ta na kujerar shugaban kasa.

 a halin yanzu akwai adadin 'yan takarar kujerar shugaban kasa 72 daga jam'iyyu daban-daban.

Kadan daga cikin su sun hadar da Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, Oby Ezekwesili ta jam'iyyar APMN da kuma Kingsley Moghalu na jam'iyyar YPP.
Akwai kuma Omoyele Sowore na jam'iyyar AAC, Sina Fagbenro-Bryon na jam'iyyar KOWA, Fele Durotoye na jam'iyyar ANN, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP,Obadaiah Mailafia na jam'iyyar ADC, Eunice Atuejide ta jam'iyyar NIP da sauransu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: