Tuesday, 8 January 2019

KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE HANA MACE SHIGA ALJANNAH KODA KUWA TANA SALLAH:-

KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE HANA MACE SHIGA ALJANNAH KODA KUWA TANA SALLAH:-

1) Duk Matar da take da aure tayi zina.
2)Duk Matar da ta Mallaki Mijinta ta hanyar asiri ko ta hanyar tsafi
3)Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna da Mijinta lafiya
4)Duk matar da ta raba mijinta da 'ya'yansa,ko ta Hanyar Asiri ko Yaudara
5)Duk matar data raba mijinta da Yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara
6)Duk matar da tayi asiri akan saukarwa kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai haila tazo mata
7)Duk matar da tasa aka daure mahaifar kishiyarta,don kar ta haihu
8)Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane
9)Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta don yayi mata kishiya.Ma'anar baka shine: Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya dawo dakin matsafiyar sai ya dawo namiji
10)Duk matar data nemi mijinta ya saketa,alhali baya cutar da ita.Kuma ba yadda ya iya
11)Duk matar da bata godewa mijinta bisa ga irin abubuwan da yake mata na Alkhairi
12)Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta
13)Duk matar da batayin wankan janaba, bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan haila ko biki
14)Duk matar da take tona asirin mijinta a cikin kawayenta
15)Duk matar da take annamimanci
16)Duk matar da take sa kayan da yake nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake fada akan irin shigar yahudawa da nasara
17)Duk matar data kara gashi akan nata
18)Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata wani abu wanda ba zai iya yi ba
19)Duk matar data dauki dan wani ta bashi Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba
20)Duk matar da zata cewa Mijinta tunda muke dakai meka taba yi mini.










 WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH
(S.A.W).

Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi amfani da. su koya sanar
da wanda zaiyi amfani dasu ???"
Sai Abu Huraira (r.a) yace Ni zan karba ya Ma'aikin
Allah.

Sai Manzon Allah (s.a.w) yariqe hannu na ya maimaita minsu sai yace;
1. "Ka guji aikata sabo, zaka zamo
wanda yafi kowa bauta a cikin mutane.
2. "Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zakafi kowa
arziqi cikin mutane.
3. "Ka kyautatawa maqobcin ka, zaka
zamo (cikakken) Mumini.
4. "Kasowa mutane abinda kake sowa kanka, zaka
kasance (cikakken) Musulmi.
5. "Kada ka yawaita dariya, domin yawan Dariya na
kashe zuciya.
@SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA
930.

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA
RIQESU KOKA SANAR DA WANDA ZAIYI AMFANI
DA SU.
IDAN KA TURAWA YAN'UWA MUSULMAI
BAKASAN WA ZAI YI
AMFANI DA SU BA, KAGA KASAMU LADAN
MUTANE MASU TARIN
YAWA.
Allah bamu iKon kiyayewa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: