Wednesday, 9 January 2019

Tofa!! Za'a haramtawa yan mata amfani da mayukan haskaka fata ( man-bilicin )

Tofa!! Za'a haramtawa yan mata amfani da mayukan haskaka fata ( man-bilicin )


Kasar Rwanda ta haramta samar da duk wani man shafawa ko sabulu mai sanya haske a kasar.

Da yawa daga cikin kasashen Afurika sun haramta samar da irin wadannan mayuka amma basu tsaurara doka akai ba
Shugaban kasar ta Rwanda ya nuna damuwar sa akan yawaitar abubuwan dake sanya hasken

Wani jami'in hukumar lafiya ta kasar mai suna Francois Uwinkindi yace " Mun mayar da hankali akan fadakar da al'umma akan wannan abu da kuma kwace wadannan kayayyaki,muna munbi bayan ragowar kasashen da suke yaki d wadannan kaya masu canja launin fata,

Shugaban kasar na Rwanda Paul Kagame ya nuna damuwar sa akan bunkasar irin wadannan kaya a cikin al'umma,

An bayyana cewa jami'an yan sanda a kasar sun fara kwace irin wadannan kaya tun a satin karshe na shekara ta 2018.

Amma da dama daga cikin masu amfani da wadannan abubuwa basuyi farin ciki da wannan doka ba inda sukace suna da damar zabawa kansu abinda sukaga zasuyi
Da yawa daga cikin kasashen Afurika sun haramta samar da ire iren wadannan abubuwa amma basu sanya doka akan hakan ba, wadannan kasashe sun hada da Ghana, Afrika ta kudu, Mali da kuma Najeriya

A shekarar data gabata ne Blac Chyna dake Amurka suka kawo wani sabon samfurin mai dake kara hasken fata zuwa kasar Najeriya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: