Wednesday, 6 February 2019

Matasa a Benuwe sun kona tsintsiya, sun wanke filin da Buhari ya yi kamfen (Hotuna)


A yayin da zabukan shekarar nan ke kara matso wa, manyan ‘yan takarar kujerar shugaban kasa na cigaba da kaddamar da yakin neman zaben su a jihohin kasar nan

A yau Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da tawagar yakin neman zaben APC su ka ziyarci jihohin Benuwe da Nasarawa

Shi kuwa a nasa bangaren, Atiku Abubakar, da tawagar yakin neman zaben PDP sun ziyarci jihohin Borno da Yobe ne
Sai dai wata majiyar mu ta sanar da mu cewar wasu fusatattun matasa da ke adawa da shugaba Buhari da jam’iyyar APC sun wanke filin da shugaba Buhari ya kaddamar da kamfen din sa. Kazalika, matasan sun kona tsintsiya tare da rera wakokin nuna kyama ga jam’iyyar APC.

Ko a kwanakin baya sai da wasu matasa a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna su ka wanke filin da gwamna Nasir El-Rufa’i ya yi taro domin nuna fushin su a kan aiyukan ta’addanci da su ka hana karamar hukumar su zama lafiya.

Ana zargin wasu ‘yan siyasa ko gwamnatin jiha, idan da banbancin siyasa tsakaninta da gwamnatin tarayya, da daukar nauyin irin wadannan matasa da ke ziyartar filin taro domin yin shara ko wanke wurin bayan tafiyar dan takara.

Akwai adawar siyasa mai zafi tsakanin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, da fadar shugaban kasa,

Dangantaka tsakanin gwamnan da fadar shugaban kasa ta yi zafi ne sakamakon barkewar rikicin manoma da makiyaya a jihar Benuwe. Wannan ne kusan silar ficewar gwamna Ortom daga APC,
jam’iyyar da ya ci zabe a cikinta a shekarar 2015.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: