Monday, 27 February 2017

Na Manta Komai Part 4

Tashin hankali baa sa maka rana,da alama dai Suhaila ta yi loosing Memory d'inta ne a yanda na fahimta,... Can kuma Ahmad, sai tunane-tunane yake shin abun nan, pritending take kamar bata san komai ba, dan yasan kissar mata yawa gareta, ko kuwa akwai wani abune?? Gani yake kamar ta amincene ta zauna da shine a matsayin mijin nata, shine take basarwa, to lallai yana ganin hakanne, ta amince ta zauna dashine dinne, yayi dan murmushi wanda ya fito da kyanshi a bayyane, kai mata akwai iyayi, kalli yanda ta fuske kamar ba itaba a bayyane yace "Mata! Mata!! ya kada kai ka barsu kawai....." Amincewa tayi dan ya zama dole, domin kuwa bakin alk'alami ya riga ya bushe, an riga an d'aura masu Aure shi da ita, kuma ba saki har abada, Ahmad kenan da masu aikin gidansu suka saka masa suna Alhaji Rabo..... Na zama mijin Suhaila kenan, yayi murmushin da bai kai ciki ba, amma azuciyarshi har yanzu inya tuna wasu abubuwa sai yaji wani baqain ciki da zuciyarshi ke tafasa, kuma har yanzu ya kasa cire wannan abu a zuciyar shi, wanda duk sadda ya tuno abin yake jin zafi har yaji ya tsaneta, amma yayi ma mahaifinta alk'awarin zai rik'eta amana a matsayin matarshi, amma ya za'ayi yayi hakan,!? bai saniba har yanzu,!! Shiyasa lokuta da yawa sai yaji Kamar yacema mahaifinta ya fasa aurenta,amma kuma sai ya kasa....!!

*************

SHEKARA UKU DA SUKA WUCE

Shekara uku da ta suka wuce,... lokacin da mahaifan Suhaila suka dawo daga umra, Ahmad tuni ya riga ya koma k'asar Holland, basu sake haduwa da Ahmad ba, dan bai sake zuwa Nigeria ba, sai lokacin da ya samu labarin rasuwar yayan shi da matar yayan shi, sun kuma bar baby dinsu Surayya Just 2month da haihuwa, yana nan gida yazo ta'aziyyar yayan shi, sati daya aka yiwa Ahmad waya aka gaya mashi ya dawo gida, domin matarshi na cikin mawuyacin hali,rabon suyi sallama, yana isa akayi mata C.S aka ciro babyn cikin ta, ita kuma ta rasu,ya sama Baby dinsa Suna Rukayyah...sunanda matarshi takeso take kuma k'auna kenan shi kuma ya saka mata Rukayyah..
********

Rasuwar yayanshi sunyi magana sosai da Alh Ibrahim mahaifin Suhaila, inda ya gaya mashi abubuwan da yawa da bai sani ba, wanda yake zaton shine yayan nashi ke cewa zai gaya mashi, Amma kuma Allah ya masa cikawa, asalin samun gonar da suke ciki yanzu kenan wadda da tana hannun yayan nashi ne kamin ya rasu, duk makircin da Alh ismail ke k'ullawa,wanda ya janyo accident d'in motar yayan shi, ya yi sanadin rasuwar yayan nashi da matar yayan shi, amma har yanzu dai ana kan bincike, dan a gano gaskiyar abinda ya faru, wannan dalilin yasa Ahmad yasa ya tattaro ya dawo gida don yaci gaba da harkar bussines din mahaifinshi da yayan nashi.!! Ba'a dade ba, Alh Ibrahim ya neme Ahmad da ya auri y'arshi y'ar autarshi Suhaila, wacce duk cikin yaran shi yafi k'aunarta sabida tsananin kama da takeyi da mahaifiyarsa. Ahmad kuwa ya kuma amince da auren Suhaila amma ya amince ne bawai dan yana sontaba hasalima ya tsaneta tun tana yarinya data mishi wani abu, kawai dan ya lura Alh Ibrahim mahaifin Suhaila mutun ne mai mutunci kuma shi kadai ya yadda dashi a cikin abokan mahaifinsa, bayan an bashi Suhaila akace kuma an bashi lokaci har sai ya shirya sannan ayi auren, ************ A ranar a aka aje maganar auren sa da Suhaila, Ahmad ya samu kanshi dayi ma duk mutanen dake aiki a gidan su Suhaila, k'ananan ma'aikatan kampanin Alh Ibrahim kyautar kud'i dubu goma goma, shi kanshi bai san dalilin yin hakan ba, sai dai kawai ya tsinci kanshi cikin farin ciki da annashuwa, dukda yasan bayason Suhaila, tun daga ranar suka sa mashi suna Alhaji Rabo wanda kowa a gidan da sunan yake kiransa Ita kuma marainiyar y'arshi da da yar yayanshi, kakarshi da nanny dinsu ne suke kula dasu, har suka dan girma, suka fara wayo kullun cewa suke yaushe za'a kawo masu Momy d'insu, hakan yasa Ahmad ya bijiro da xancen auren Suhaila, amma badan yana sontaba, Su kuma yaran ganin Suhaila yasa suke tunanin mamansu ce, ga kuma madam din TA MANTA KOMAI. Sabida lokacin da zai tafi daurin auren haka yace masu zaije ya kawo masu Momy dinsu....
**************

Cikin dare Suhaila ta farka cikin bacci amma ta kasa motsi,gabanta ya fadi ita da ta kwanta a palo, miya kawota daki, al'amarin ta fa sai d'ad'a jagule mata yake! "Waima ina mijinta ne!?" Yayanta ne gabanta, Surayya ta rungumeta a dama Rukayyah a hagu...tayi murmushi ta k'ara rungumesu, babu shakka y'ay'anta na sonta, ashe suma sun farka cikin darene suka dawo wajenta, gaskiyayarane kyawawa babansu kyakykyawane, Itama ba daga baya ba, ai kuwa dole su bada result mai kyau da haka bacci mai d'ad'i ya k'ara kwashe ta.....
.
kira da Dady, itace yarinya ta hud'u kuma itace Auta, Dady yana matuk'ar sonta ne sabida tsananin kama da sukeyi da mahaifiyarsa. Asalinsu buzaye had'e da fulani, Alhaji Ibrahim murzajjen d'an boko ne, irin masu tara suma dinnan aka, yazo birni gun wani aiki na idanu, a k'auyen Tambuwal cikin birnin Sokoto inda yaga gari ya masa sai ya dawo nan da zama, anan k'auyen ya hadu da mahaifiyar su Suhaila, har suka yi aure, ta haifa mishi yara hud'u mata biyu maza biyu. Rukayyah itace babba, sai kuma Al- Ameen sai Suhaila da Suhail wayanda su twins ne, sune k'anana. Harkar gyaran ido ta karbeshi ba kadan ba, inda ya koma birnin Sokoto da zama, anan ya had'u da Alhaji Isma'el, da kuma Alhj Sulaiman sai aka koma kasuwanci. Alhaji Sulaiman shine mahaifin Su Ahmad, yaransa biyar Mahmoud shine babba, sai Zainab, sai kuma Ahmad da Fatima, sai autarsu Khadija. Sun shaqu iya shak'uwa su ukunnan, tare suke duk wata harka ta kasuwanci.
.
*********
Wata rana Ahmad ya dawo daga makaranta sai ya hango kamar ana butsul-butsul a ruwa, har ya wuce sai kawai ya dawo yana lek'awa sai yaga abin yayi yawa, koda ya matso sai yaga mutum ne, baisan lokacin da ya fada cikiba ya tsamota. Yarinya ce 'yar kimanin shekara 8, ya kwantar da ita ya rik'a matsa mata cikinta a hankali tana fitar da ruwanda tasha baki hanci, har ta fara tari, ta bude ido a hankali, sai ta sake rufewa, Ahmad dai yaga abin ba nashi bane sai ya d'auketa ya kaita gidansu, mamarshi na ganinta ta fara salati, da yake ita tasan ta, "ina ka samo Suhaila ?? " Yama Ammi bayani, " ai banga ta zama ba" ta dauko mayafi ta yafa ta sungumi Suhailah sai gidan Alhaji Ibrahim ta maida musu bayanin komai, Anata godiya, bayan kwana biyu Suhaila ta ware waras, Mama ta kirata, "Ke wai garin ya kika fad'a ruwa?" "Ba wannan ne ya turaniba!" Cikin rashin fahimta Mama ta k'ara tambayarta, "wanene wannan?" Suhaila kuwa ta tsaya kai da fata akan Ahmad ne ya jefata ruwa, Mama cike da mamaki, take jimamin lamarin, sai da Dady yazo ta mishi bayani abin da Suhailah ta gaya mata, shikan bai yardaba sam, dan yasan halin Ahmad tsab, dan haka bai d'auki maganar da mihimmanci ba, mama ta yafa taje ta sami Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Ahmad ta bata labarin da Suhaila ta gaya mata, tace kawai a jawa Ahmad kunne kada ya k'ara aikata irin haka, an kuwa yi sa'a Ahmad yana gida, "kai Ahmady" na'am ya fito d'akin su, cikin girmamawa ya gaida Mama, ta amsa a sake, "dama Suhaila ce tace wai kai ka jefata ruwa ranar " "waye Suhaila Ammi!?" Ya tambaya "yarinyar da ka kawo shekaran jiya kace ta fad'a ruwa mana, har ka fito da ita" shiru yayi chan kuma yace "akan me zan jefata ruwa Ammi? Mi ta mini da zan jefata ruwa?" " mudai yanzu ba wannan ne gaban mu ba, kawai ka fita harkar yarinyar nan idan ba zaka taimaketa a matsayin k'anwarka ba, to kuwa ka rabu da ita" Mama tace "kai tashi ka tafi abinka, kilama shiririta ce irin ta Suhaila" cike da mamaki ya wuce d'akin shi, lokacin Ahmad yanada shekara sha biyar, amma akwai natsuwa gun shi, gashi komai nashi a tsare, iyayen sukaci gaba da hirar su. Tun daga wannan rana Ahmad ya d'auki tsanar duniya ya d'aurawa Suhaila, gashi ba wani saninta yayiba dan ko ganinta yayi bazai ganeta ba, amma ko sunan ta bayason ji wannan kenan....

Da yake su uku suke kasuwancin su komai yana tafiya yanda ya kamata duk da cewa Alhj Sulaiman shine shugaba, dan kusan 50%(rabin dukiyar kaauwanci) dukiyar shi ce, sauran rabin kuma na Alhaji Isma'el da Alhaji Ibrahim ne. Alhaji Isma'el ya d'auki ki'yayyar duniya ya d'aura musu ba tare da sun saniba, anan ne yayi nasarar lik'awa Alhj Ibrahim satar kudin company kusan M.200, kuma akayi bincike akaga kudin gurin Alhj Ibrahim, wanda duk sharrin Alhj Isma'el ne, ba tare da wani dogon bincike ba suka cireshi a shikinsu, suka dawo su biyu. Abin yama Alhaji Ibrahim zafi ba kad'an ba, sharri harma na sata, gashi da zuciya kamar me, bak'in cikin haka yasa yabar Sokoto ya dawo Katsina da kasuwancin sa.
.
******************
BAYAN SHEKARA DAYA.
Alhaji Ibrahim yazo Sokoto ganin gida da iyalinsa anan ne Suhaila ta sami accident ta fito daga gidan yayar ta Rukayyah itada Suhail mota ta kad'e ta, shima Ahmad ya fito gun wani cafe yaga mutane, yana zuwa yaga taro, ba abinda akayi mata gata kwance, shida wani bawan Allah suka samo taxi da police aka kaita asibiti, duk da ko lokacin bai ganeta ba kuma bai kiyaye fuskar taba, wannan bawan Allah ya gano iyayenta da taimakon suhail. Dady ya riga ya koma Katsina, yace Rukayyah ta kula da ita dan ayyuka sun masa yawa, an mata duk abinda ya dace.
.
Kullum Ahmad yana zuwa dubata, duk da baisan wacece itaba, ranar ta tashi ta mik'e zaune yana zaune yana karanta wasu takardu Anti Ruky na sak'a, dan mayyar sak'a ce, tayita kallonsa, suna hada ido, sai ta masa murmushi, tace " inasonka kaji " shima ya mata murmushi, yace " nima inasonki" ta k'ara murmushi har haqoranta da take 6an6ara suke bayyana "to zaka aureni idan na girma irin na Anti Rukayyah da uncle?" Yace "Eh mana" yeeeee tace sannan taci gaba, " to kaga Anti Rukayyah tana cema uncle Honey, ni mi zaka cemini!?" "Aike kyakyawa ce so zan rik'a kiranki da beautiful" ta zunburo baki "ni banason sunan, ko Dady Some times (wani likaci yana cemin beauty, fadi wani mai d'ad'i" ta ya mutsa fuska a yangace irin na yarinta, "kina son Dear" a haf, ta d'auke kai gefe, tace "ai ko mama tsohuwa dear take cema Dady" dariya yayi sosai har fararen hak'oransa suka bayyana.....

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: