Tuesday, 19 February 2019

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

A yau, Talata, ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga halin damuwa bayan shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin gudu wa da akwatin kuri’u a zabukan da za a gudanar cikin watan Fabarairu da Maris.

Fadar shugaban kasa ta ce kalaman shugaba Buhari gargadi ne ga ‘yan siyasar da su ka mayar da satar akwatun kuri’u ta hanyar amfani da ‘yan daba al’ada a lokutan zabe.

Da ya ke Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, y aba boyayyen abu ba ne cewar wasu ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin su sace akwatin kuri’u sannan su kashe ma su kada kuri’a ko kuma su raunata su.

Ya ce shugaba Buhari ya yi kalamin ne domin tabbatar da cewar ba a cutar da ma su kada kuri’a ba lokacin zabe tare da bayyana cewar ya kamata a jinjina wa Buhari bisa wannan gargadi ga ma su niyyar sace akwatin kuri’u a lokutan zabe


Kazalika, ya nuna rashin jin dadin sa bisa sukar Buhari a kan furucin da ya yi a kan ma su niyyar sace akwati, tare da nuna mamaki a kan dalilin damuwar su da kalaman na shugaban kasa.

A cewar Shehu, “ mambobin jam’iyyar adawa, musamman jam’iyyar PDP, ne ke sukar Buhari saboda sun gama shirya yadda za su yi magudin zabe ta hanyar satar akwatin kuri’u .

“ Sun fahimci cewar shugaba Buhari ba zai lamunci almundahanar da su ka saba da ita ba wannan karon. Sun nuna abinda su ke niyyar aikata wa, ” a cewar sa.
Shehu ya bayyana cewar duk wanda bashi da wata mummunar manufa a kan zabukan da za a gudanar, kalaman Buhari ba za su dame shi ba.

A cewar sa, “ kalaman Buhari ba za su tayar da hankalin duk mai son a yi zabe sahihi kuma mai tsafta ba. ”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: