Friday, 15 February 2019

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a babbar gadarnan ta Ebonyi

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a  babbar gadarnan ta  Ebonyi


Rahotanni sun kawo cewa an kama wasu mutane biyu a jihar Ebonyi yayinda suke dana bam, a gadar Idembia da ke karamar hukumar Ezza South na jihar.

Gwamna David Umahi ya bayyana hakan a wani jawabi na musamman kan lamarin tsaro ga mutanen jihar a ranar Juma’a, 15 ga watan Fabrairu.

Yace kamun ya biyo bayan rahotannin kwararru cewa wasu mambobi na wata jam’iyyar siyasa na shirin dana bam a kan gadar da wasu wurare a jihar.
Yace wasu mazauna kauyen da ke kusa da gadar wanda ya sada Ezza South da karamar hukumar Ohaozara ne suka kama mutanen biyu.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa dan takarar kiujerar majalisar dokokin kasa na wata jam’iyyar siyasa, yan kwanaki da suka shige ya je wani waje a jihar domin siyan bama-bamai amma masu aiki a wajen suka ki amsa bukatunsa inda suka sanar da gwamnatin jihar

A wani lamari na daban, mun ji cewa kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: