Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC za ta dauki hayan jakuna da kekunan hawa domin amfani da su wurin rabar da kayayakin zabe a wuraren da ke ta wahalar zuwa a wasu sassan jihar Gombe.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishinan zabe na jihar, Alhaji Umar Ibrahim a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Gombe a ranar Juma'a.
Ibrahim ya ce wuraren da ke da wahalar zuwa a suna kauyuka ne da ke kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Shingom duk a jihar ta Gombe.
"Za mu dauki hayan jakuna da kekunan hawa da babura domin rabar da kayayakin zabe
"Hakan ya zama dole ne saboda rashin hanyoyin mota shiyasa INEC tayi tanadi da shirye-shiryen yadda za a isar da kayayakin zabe zuwa wuraren," inji shi.
Ibrahim ya ce hukumar tayi tanadi da ya dace a fanin samar da tsaro kuma ta wayar da kan masu kada kuri'a.
Ya kuma ce anyi tanadin takardun kada kuri'a na brail da makafi za suyi amfani dashi kuma kutare suna iya amfani da kafarsu domin dangwala zaben.
Har ila yau, Ibrahim ya kuma ce hukumar zaben tayi tanadin gilashi mai kara girman abubuwa ga wadanda ke fama da ciwon ido saboda su kada kuri'an cikin sauki.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa kwamishinan zaben ya ce hukumar ta tanadi na'urar da za tayi amfani da shi domin ganin yadda zaben ke tafiya tare da kuma samar da mutane masu sanya ido a kan zabe.
0 comments: