Monday, 27 May 2019

AMFANIN DABINO A JIKIN DAN ADAM Musamman A watan Ramadan


Dabino na da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun a da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna. Wata malama mai zurfin ilimi a bangaren kayayyakin abinci a Juddah, wato Prof.


 Waddaha Mohammed na cewa, Cin kwayan dabino guda goma mai nauyin 100g zai iya ba mutum wasu abubuwa na amfani ga lafiya jiki. Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium. Ana kimanta zakin sukarin da dabinon ya tattara wajen kashi 78-70 cikin dari na abubuwan da dabinon ya kumsa, kuma wannan sukarin na dabino nan take ya ke narkewa a cikin jini sabanin sauran 'ya'yan bishiya. A nan ne za mu ga hikimar muslunci ta sanya dabino ya zama abin farko da mai azumi zai fara ci,

 wannan don a dawo masa da abubuwan bukatar da ya rasa ne cikin gaggawa, Allah Mai girma ne a dukkan lamarinsa. Ba wannan kadai ba akwai ma 75g na carbohydrate, 63g na sukari, 8g na Dietary fiber, 0.4g na Fat, 2.5g na Protein, 21g na ruwa,0.262 mg na Manganese, 1.32 na minerals. 

 Abin da Prof. Waddaha ta ce shi ne bushasshen dabino ya qumshi: Carbohydrate 79.6%, Fat 2.5%, Water 33%, Minerals 1.32%, Dietary fiber 10%, sai Vitamins A, B1, B2 da C, kamar yadda ya kuma ya kumshi abubuwa da dan dama, a takaice in ka duma dabino shi kadai ya isa ya zama abincin da zai gina jiki in ba don tsoron a yi masa cin koshi ba. Bincike ya nuna cewa dabino ya kumshi sanadaran; Minerals da Calcium, da Protein, da Fat, da Lime, da Coramine, da Dietry fiber, da Phosphor, da da Chlorine, Manganese, da Potassium, da Copper, da Vitamin C, da kuma Magnesium. Da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kumshi manya-manyan abubuwa na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya, suma bayyana wa mutum matasantarsa ko da kuwa ya dan kwana biyu, da za a haga dabino da madara tabbas abinci ne mai kyawun gaske, masamman ga wanda yake da matsalar ciki. 

Masana kimiyya na cewa, abubuwan gina jiki da su ke cikin danino na daidai ne da na wani nau'i na nama, ko ribi uku na kifi. Kuma ya kan amfanar da masu cutar fatarar jini, da wasu cututtuka da suka shafi kirji kamar yadda ake kwaba shi a dafa a rika sha daidai gwargwadon yadda aka nunawa mutum. Dabino na amfanar da kananan yara, da matasa, da 'yan wasa, da ma'aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: