Sunday, 16 April 2017

LABARI MAI DADI: Farashin shinkafa zai fadi zuwa N6000, an bayyana ranar da za’a fara siyarwa

Manoman shinkafar gida sun sanar da cewa farashin shinkafa zai sauka zuwa N6000 - Manoma na cikin shirin masu karban bashi daba CBN don kara samar da wadataccen abinci - Bukatar shinkafar gida ya karu.
Ana saka ran cewa farashin shinkafa zai fadi zuwa N6000 a cikin watanni shidda masu zuwa a cewar Alhaji Aminu Goronyo wanda ya kasance shugaban kungiyar manoman shinkafa na Najeriya (RIFAN).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Goronye yayi magana a karshen mako inda yace manoma sun tsananta samar da shinkafa da wannan ne farashin shinkafa zai sauka.

Yace ayanzu aka siyar da shinkafa kasa da farashi N10000 a wasu jihohin arewa sannan kuma cewa yawan bukatar shinkafar ta shafi manoma ta hanya mai kyau.

Arewarmu.com ta tattaro inda Shugaban kungiyar na RIFAN ya bayyana cewa manoma da daman a amfani da damar shirin bayar da bashi da babban bankin Najeriya (CBN) keyi sannan kuma cewa kungiyar san a daukar manoma da dama don su shiga shirin.

Ya ce yana sa ran farashin shinkafa zai ci gaba da sauka don yan Najeriya su samu damar siya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: