Wannan wani takaitaccen bayani ne akan binciken da muka gudanar akan ALBASA irin wannan wacce ake nomawa kuma muke ci a nan kasar Hausa.
Allah (SWT) yana cewa:
“HAKIKA A CIKIN HALITTAR SAMMAI DA KASSAI DA KUMA JUYAWAR DARE DA RANA AKWAI ABIN LURA GA MASU HANKALI”.
“SUNE WADANDA SUKE AMBATON ALLAH A TSAYE, DA KUMA A ZAUNE, DA KUMA A KWANCE A KAN HAKARKARINSU. KUMA SUNA TUNANI A CIKIN HALITTAR SAMMAI DA KASSAI, (SUNA CEWA) :
“YA UBANGIJINMU! BA KA HALICCI WADANNAN (ABUBUWAN) A BANZA BA…”
To idan mun duba za mu ga cewa wannan ayar tana ishara ne garemu cewa MU YI TUNANI, MU YI BINCIKE A CIKIN HALITTUN ALLAH.
Kuma Hakika akwai wasu boyayyun Ilimai a cikin dukkan abinda Allah ya halitta, da wanda muke gani da wanda ma bamu iya ganinsu.
Saboda dogaro da wannan ayar ne muka kuduri aniyar yin bincike akan abubuwan da muke ci a cikin abincinmu na yau da kullum domin ganowa irin fa’idojin da suke kunshe a cikinsu.
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“KU NEMI MAGANI YA KU BAYIN ALLAH! DOMIN ALLAH BAI TABA SAUKAR DA CUTA BA, FACE SAI YA SANYA MAGANINTA”.
(Abu Dawud ne ya rawaito shi).
Idan mu ka dauki ALBASA kadai irin wannan ta mu ta kasar Hausa wacce a turance ake kira da “RED ONION” za mu ga cewa tana kunshe da manyan fa’idoji wadanda za su magance mana wasu daga cikin manyan cututtukan da muke fama dasu. Kuma Allah ya yi haka ne domin tausayawa a garemu.
Albasa tana kunshe da sinadarai masu yawa. Irin su Protein, Calcium, Vitamin A, Vitamin B, Vitamin C, Vitamin E, Da kuma wani sinadarin mai suna Allicin.
Shi wannan ALLICIN din shi ke haddasa idanun mutum ya ke hawaye, a duk lokacin da ake yanka albasa.
Danyar Albasa wacce ba a dade da tonota ba tana maganin kwayoyin cutar Bacteria, Hypertension, Tarin fuka, tarin Mura, har ma da ciwon koda da dai sauransu.
ALBASA tana maganin Kaduwa, Suma, Farfadiya, Ciwon Zuciya, Ciwon Ciki, Ciwon sikari, cutar Asma, olsa, da sauransu. Musamman ma idan an gaurayata da tafarnuwa.
AMFANI DA ALBASA WAJEN SAMAR DA WARAKA
1. Mutumin da ya fadi ya suma, idan aka samu albasa aka fere aka sanya masa a kofar hancinsa guda, Insha Allahu kamshinta zai sa ya dawo cikin hayyacinsa ta hanyar wattsakar da hanyoyin numfashinsa.
2. Don haka ne ake so Majinyatan da suke fama da Matsalar HEART ATTACK su rika yawan cin ‘Danyar Albasa a cikin abincinsu na yau da kullum.
3. ALBASA tana maganin ARTERIOSCLERIOSIS (wato daskarewa ko kekashewar manyan jijiyoyin cikin zuciyar Dan Adam, da manyan hanyoyin jinin da suka Turowa jini da kuma janyoshi daga zuciyar Dan Adam).
4. Don haka tana magance BLOOD PRESSURE kuma tana Qara taimakawa wajen blood circulation (zagayawar jini a jikin Dan Adam).
5. MASU CUTAR DIABETES (Ciwon Sikari): Su samu Lansur mai kyau, a wanke shi sosai, sannan a yayyanka shi, a samu garin karago (kuli-kuli) cokali 3 tare da garin hulba cokali guda da rabi a barbada wannan garin, sannan a samu katuwar albasa (‘Danya) a yanka a ciki. Insha Allahu wannan abincin idan kana ci kamar sau 2 a sati guda, zai zabge maka Sikarin da ke cikin jininka, kuma zai kore maka Cholestrol daga jikinka.
6. Wanda ya ke fama da ZAZZABI, ko Mura, ko ciwon makogoro (makoshi) Ya samu zuma rabin kofi ya yanka katuwar albasa mai kyau a ciki, sannan ya cinye tare da zuman. Insha Allahu zai samu lafiya da gaggawa.
7. Hakanan mai fama da olsa, ko jin zafi a lokacin fitsari, shi ma idan ya ci wannan hadin zai samu waraka sosai.
8. Idan mutum yana fama da ciwon goshi ko ciwon kai na gefe daya dinnan, a samo albasa a kirba ta tare da tafarnuwa sannan amanna masa akan goshinsa ko daidai wajen ciwon kan.
9. Wanda zuma ta harbeshi, ko cinnaka ya cije shi, ko kunama ta harbeshi, idan aka manna masa irin wancan hadin sannan aka daure wajen kamar bandeji, shima zai samu waraka da izinin Allah.
10. Wanda yake fama da habo (zubar jini daga hanci) idan aka sanya masa dakakkiyar albasa yana shakar warinta insha Allah jinin zai tsaya.
11. Wanda yake fama da matsalar INDIGESTION (rashin narkewar abinci) shima idan ya ci danyar albasa zai samu waraka da izinin Allah. Domin albasa tana taimakawa jikin Dan Adam wajen samar da Sinadaran da suke narkar da abinci.
12. Wanda wuta ta kona shi, idan aka kirba albasa aka manna masa a wajen, zai ji zafi sosai, amma kuma wajen zai bushe da wuri kuma zai warke cikin kankanin lokaci.
13. Cin danyar Albasa kullum yakan zama riga-kafi ga mata na Sankaran mama da ta mahaifa da kuma sauran cututtukan da suka shafi mahaifan mace (diseases of the womb).
Daga Zauren Fiqihu; zaku iya ajiye tambabyoyinku a kasa

0 comments: