Saturday, 15 April 2017

Yadda Za'a Magance Matsalan Warin Baki Cikin Sauki

A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku lura da hakorinku, wato- cire dattin hakori da kuma kara wa hakorinku fari da kuma lafiya.

Ana so ku rika wanke bakinku da man goge baki ko aswaki akalla sau biyu duk rana, hakan zai sanya hakorinku ya yi haske.
Idan kana da dattin hakori sai ka nemi man goge baki kamar daya daga cikin wadannan: Colgate da Rembrandt da 3D Crest da Listerine da Akuafresh da sauransu, sannan kuna goge hakorinku da shi.

Za ku iya amfani da bakar soda (Baking Soda) wajen goge hakorinku sau biyu a mako. Kadan ake so ku rika diba idan za ku yi amfani da sodar. Sannan bayan haka ana bukatar ku kuskure bakinku sosai bayan kun kammala amfani da sodar. Kada don kuna amfani da wadannan sinadaran sai kuma ku daina goge bakinku kamar yadda ya kamata.

Ku rika amfani da kororon da ake shan jus ko lemon kwalba wajen shan jus ko lemon kwalba, hakan zai kara wa hakorinku fari da haske. Ya kamata ku rage yawan shan kofi da kuma shayin da ba a hada da madara da sauran kayan hadi ba, domin rashin yin hakan zai kara wa hakorinku datti. Ku guji shan abu mai tsananin sanyi ko zafi, hakan zai taimaka muku wajen kara hasken hakorinki. Ku guji yawaita shan abu mai siga domin kauce wa rubewar hakori.

Ku rika amfani da tsinken sakace hakori bayan kun ci abinci, musamman idan kun ci nama ko kifi da dai sauransu. Rashin yin hakan zai sanya sauran abinci ya taru a matse-matsin hakorinki, wanda kuma zai iya janyo wa hakorinki rubewa ko kuma ya yi duhu, ko ya haifar muku da warin baki.

Allah yasa mu Dace....
Zaku iya ajiye tambabyoyinku a kasa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

5 comments:

  1. Assalamu Alaikum.
    Allah ya sakamuku da Alkhairi.
    Pls ina fama da warin baki sosae,don wallahi nima yana takuramin da warin sosae amma sae daevduk na dauki matakan da zan iya amma har yanzu yana nan, sae dae gaskiya bani da abubuwan da kuka lissafo a wancan posting din naku.
    Bani da ulcer, kuma bakina baya bushewa
    again nakan wanke bakina one times a day sae dae wani time din nakan wanke sau biyu.
    again na taba zuwa hospital aka kankaremin datti kuma na samu shawarori daga wajen kananan likitocin akan yadda zanke, harma akaban shawara ina amfani da mouth wash, kuma inayi amma gaskiya still bakin yana warin sosae.
    pls dan Allah idan da wani hanyar da zae daena warin ku taemakamin da ita dan Allah.
    wallahi banajin dadin rayuwana.

    ReplyDelete
  2. Ameen, gaskiya wanke baki sau daya gamai warin baki iri naka bazai magance maka wannan matsala ba ya kamata ace kullum ka wanke sau uku ko fi kuma ka nemi medicated marclean kana amfanin dashi.

    ReplyDelete
  3. Muna godiya kwarai Allah yasaka muku da alkhairu
    Kuma ya Kara himma da hazaka

    ReplyDelete
  4. Dan Yaya zanyi in magance kurajengaba wato kuraje ne Yan kanana suka fito min akewayen kaciyata.
    Kuma I tried magunguna da yawa Amma har yanzu ban dace ba.
    Dan Allah ataimaka mini.
    Nagode.

    ReplyDelete
  5. Muna godiya kwarai Allah yasaka muku da alkhairu
    Kuma ya Kara himma da hazaka

    ReplyDelete