Tuesday, 18 April 2017

Su Waye Suka Mallaki Makudan Kudaden Da EFCC Ta Gano?

‘Yan Najeriya na ci gaba da maida martani game da cece-kucen da ake yi game wasu marayun kudade kimanin Naira Miliyan 250 da Hukumar EFCC ta sake kamawa sakamakon kwarmaton da masu fallasa bayanai suka yi a birnin Ikko, yanzu haka masana na ganin akwai abin dubawa.

Kudin sun kunshi Yuro dubu 547 da 730 da kuma Fam dubu 21 da 90 da kuma Naira miliyan biyar da dubu 648 da 500, wanda idan aka hada jimmillar kudin ta kai kimanin Naira Miliyan 250.

To sai dai kuma yayin da ake cece-kuce game da kowa ye ya mallaki kudaden, yanzu haka kungiyoyi da masana sun fara maida martani tare da yin kira ga shugaba Buhari, yayi bayani wa ‘yan Najeriya game da makudan kudaden da Hukumar EFCC ta gano.

Abdullahi Prembe, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa, yace akwai abin dubawa game da wadannan kudade.

Wasu dai na danganta wannan lamari da sa-toka-sa-katsin dake faruwa game da batun tabbatar da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar EFCC, lamarin da ake ganin akwai hannun wasu na kusa da shugaban kasa, batun da Mallam Umar Dan Kano, dake zama mataimakin shugaban kungiyar yan jaridu ta NUJ, yace kamata yayi gwamnatin kasar ta fitar da Jama’a daga cikin duhu a daina boye-boye kowa ya gane wanda ya mallaki wadannan kudi koda kuwa yana cikin gwamnati.

Yaki da cin hanci da rashawa na cikin kudurorin gwamnatin Buhari, wanda kuma da alamun kwalliya na biyan kudin sabulu. Koda yake akwai bukatar karatun ta natsu.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: