Wednesday, 19 April 2017

Kannywood: An Gano Manyan Jarumai Bakwai (7) Dauke Da Cutar Kanjamau

Wannan wani sabon labarine wanda wakilin mu Muhammad Lere ya samo mana shi jiya. Wani abin Allah ya kyautane ya faru jiya

Domin wasu jarumai su bakwai aka gano suna dauke da kwayar cutar kanjamau (HIV/AIDS) Idan za ku iya tunawa a watannin baya mun kawo maku yanda cikin jarumai ya duri ruwa a lokacin da aka sami wata jaruma wadda ta fito a fim din "Teburin Mai Shayi" tana da kanjamau.

Arewarmu.com ta samu labarin daga majiyar mu cewa To, yau gashi an wayi gari jarumai bakwai duk suna dauke da cutar kanjamau. Wannan labarin ya tayar da hankali sosai.
Sabida yanda abin ya shafi manyan jarumai. Tun adaren jiya aka ga fuskokin wasu jarumai a asibitin Murtala dake Kano State, sabida su tantance lafiyarsu.

A bayyana sunan jaruman da abin ya shafa. Kuma mu san su amma shuwagabannin kungiyar kannywood sun hana a bayyana sunayen su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: