Wednesday, 3 May 2017

Kiwon Lafiya: Abubuwa Uku Dake Kawo Warin Baki


Likitan hakora Shola Adeoye ta ce sakamakon rashin kula ne da hakora ne yak e kawo warin baki
Ta fadi hakan ne yayin da take hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Ibadan.

Ta yi bayanin cewa mutane da dama na fama da warin baki ba tare da sun san cewa bakin nasu na irin wannan wari ba wanda hakan ke hana kan ya mai fama dashi cikin rashin jin dadi da walwala.

Adeoye ta ce za a iya gane cewa ko baki na wari idan mutum ya lashi bayan hanunsa sannan ya sunsuna.

Ta ce idan da wari ya kamata mutun ya je asibiti domin a wanke masa ko mata domin samun lafiya akan hakan.

Bayan haka likitan ta ce akai wadansu hanyoyin da ke sa a kamu da irin wannan matsala na warin baki da ya hada da:

– Kamuwa da cutar dake kama makogwaro da kuma hanjin cikin mutum.

– Shan taba Sigari

– Bushewar baki.

Adeoye ta shawarci duk wanda ke fama da irin wannan matsalar ya gaggauta zuwa asibiti domin a wanke masa hakora sanna a dinga tsaftace baki da wanke harshe idan anzo wanke baki.

Daga karshe ta ce idan har bayan wankin hakoran warin bakin bai daina ba mai yiwuwa ne matsalar daga wani bangaren jikin mutum ne wanda ke bukatan a ga likita.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: