Friday, 5 May 2017

Cututtuka Bakwai (7) Da Abarba Ke Magani

Abarba na maganin illoli da dama

1. Cutar Ataraitis
Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai damun gabbai da jijiyoyi inda su ke kumbura har su hana mutum sakat. Yawan shan abarbara na maganin wannan ciwo.

2. Cancer Abarba na maganin cutar ‘kansa’ mai lahanta kwayoyin garkuwa saboda sinadarin da ya kunsa na bitamin A da C da sauran su

3. Sanyi da mura Ina mai fama da tari da mura? Ya yawaita shan abarba domin kuwa yana kunshe da wasu sinadarai da ke kashe majina.

4. Karfin hakori
Kadan daga aikin Abarba akwai kara karfin jijiyoyin hakori har da ma kuma gyara suma watau gashi na jikin mutum.

5. Kaifin gani
Haka kuma abarba na kara kaifin idanu don haka mai shan abarba zai dade da idanun sa garau ko ya tsufa.

6. Hawan jini
Abarba na kare cutar hawan jini saboda sindarin ‘Pottasium’ da take dauke da shi mai amfani wajen yawo da jini a jikin mutum.

7. Abarba na hana tsufa
Ba gyara idanu kurum ko da an tsufa ba, abarba na kare mutum daga irin cutar dimuwa da sauran cututtuka na tsufa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: