Sunday, 8 July 2018

KO KUN SAN KADAN DAGA ABUNDA YAKAN FARU YAYI SANADIN DA AKAN HAIFI MATA-MAZA (wato shi ba mace ba kuma ba namiji ba) ?

To ku saurara kuji wannan abun mamaki.
Kwanakin baya na yi bayani kan yanda akan haifi da namiji da kuma yanda akan haiFi 'ya mace.
To A yau kuma zan yi bayanin kadan daga yanda ke kasancewa ya zama an haife wanda yake shi mata-maza ne.


To mata maza dai halittan mutum ne wanda in ka ganshi da ido ba za ka iya gane namiji ne shi, ko mace ba,  domin kuwa yana dauke da halittan mata da maza a jikinsa. Kamar su nono, azzakari da kuma farji kai wanin ma harda yin haila.
To a yau ga bayanin kadan na yanda lamari ke haifar da faruwan hartakai ga ana haifi irnwannan cikin ikon Allah.


akwai wadansu dalilan da kan haddasa hka baya ga rabewar kwan mace kafin haduwarsa da na namiji.
Kadan daga abinda zan fada game da haihuwar mata-maza,

samuwar mata-maza Haka na faruwa ne yayin jima'i lokacin da kwan namiji da na mace suka hadu suke ba da halitta ta namiji ko mace, to a lokacin ake samun matsala ta yadda kwan mace kafin ya hadu da na namijin da ke cinta kan rabe gida biyu; idan aka yi rashin sa'a maniyyin namiji guda biyu suka hadu da rababben kwan na mace, shi ke nan sai a samu
mata-maza . . . . . . . . . . . ."

Alhamdulillahi yanzu Cigaban zamani dai ya zo da abubuwa da dama, ciki har da dabarun sauya halittar dan-Adam ko yi mata kwaskwarima.
Don haka ne ma idan mata-maza na sha'awa za a iya yi masa tiyata a mayar da shi namiji sak ko mace sak.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: