A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA'I GUDA UKKU
Na farko 1
Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.
Idan kudinsa ya ragu xai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.
Na biyu 2
kullum yana cin arxikin Allah in halal yaci xa'a tambaye shi in haram ne xa'ayi masa axaba akai bai san karshen hisabin mai xai kasanceba.
Na uku 3
kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda yadamu da duniya Bai san makomarsa ba shin aljannace ko wutace.
GASKIYA
Babu abunda xai amfaneka sai sallarka/ki
wanda yabar karatun Alqur,ani tsawon kwana uku ba tare da uxuriba sunansa MAQAURACI wanda ya qauracewa Alqur,ani kenan.
Duniya kwana 3 ce
Jiya: munganta baxata dawoba
Yau: muna cikinta baxata dauwama ba xata wuce
Gobe: bamusan ina xamu kasanceba.
ka gaisa da mutane, kayimusu afuwa kayi sadaka domin ni da kai dasu duk Matafiyane bissalam.
0 comments: