Monday, 13 August 2018

Bamu Da Wata Alaka Da Saraki - EFCC

Hukumar EFCC, ta mayar da martini a kan maganar da wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Bukari na cewar, hukumar da wasu hukumomin tsaron kasar nan na gudabar da aiyyukansu ne don taimakawa shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.
Babafemi Ojodu, mai ba shugaba Buhari shawarar a kan harkokin siyasa ya yi wannan zargin a wata mukala daya rubuta. Zargin cewa, hukumomin tsaro na yi wa shugaban majalisa aiki ya sito fili ne a makon daya gabata bayan da jami’an hukumar DSS suka mamaye majalisar kasa.

Yayin da ‘yan nijeroiya da dama ke ganin mamatyar yana da nasaba da kokarin tsige Bukola saraki da karfin tsiya, wasu musamman bangaren shugaban kasa na ganin hukumar DSS sun aiwatar da abin da sarakin ya zana musus ne kawai. Mista Saraki ya yi watsi da wannan zargin gaba daya, yab kuma nemi a kori shugaban hukumar DSS, Lawal Daura.

EFCC ta bayyana haka ne a tab akin jami’in watsa labaranta, Wilson Uwujaren, a ranar Lahadi, y ace, lallai hukumar bata wani aiki da Mista Bukola saraki..

“An jawo hankalin hukumar EFCC, a kan rubutun da Sanata Babafemi Ojudu, mai ba wa shugababn kasa shwarar a kan siyasa inda ya yi kokarin cewa, abin daya faru wani shiri ne na shugaban majalisar dattijai na yi wa mulkij shugaba Buhari zagin kasa, in har haka ne a she mamaye majalisar dokoki na jihar Binuwai da kai hari ga masu shari’a a cikin dare da kulle hanyar shiga da fita a gidan shugaban majalisa da kuma garkuwa da Boy Dino da kulle aususn ajiya na gwamnatin jihar Binuwai kuna duk aikin Oloye”.

“Hukumar tana mai bayanin cewa, babu wani binciken karya da za a sanya ta,rufe asusun gwamnatin jihar Binuwai da na Akwa Ibon sakamakon aiki tukuru na tsawon lokaci, abon da yakamata mutane su gane kenan.

“ya na da mutkar mahimmanci mutane su gane cewa, hukumar EFCC bata da ani alaka da Bukola saraki”.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: