Sani Sadiq ya kasance shaharen dan wasan fim din Hausa, daya daga cikin jaruman da ake damawa da su a harkar fim din Hausa. An haife shi a unguwar Gangare, karamar hukumar Arewacin Jos (Jos North) dake jihar Plateau a ranar 2 ga watan Fabrairu, shekara ta 1981.
Ya kammala karatun sa na firamare da sakandare a Gangare Jos. Daga nan, ya tafi jami’ar Jos, inda ya samu kwalinsa na difloma a karatun jarida. A 2004 Sadiq ya fara harkar fim.
Ya zamo tauraro ne a shekara ta 2012.
Jarumin ya amshi lambar yabo a matsayin jarumin jarumai na Kannywood a shekarar 2012. Zuwa yanzu, ya fito a cikin fina-finai akalla guda 50.
Sadiq na godiya ga Allah bisa nasarorin sa. Sadiq ya fito a fina-finai kamar su Maryam Diyana, Adamsy, da kuma Yan Uwan Juna. Da yake magana game da godiyarsa ga Allah da ya bashi aikin da ya daukaka shi, Sadiq ya ji dadin cewar ya yi karatu a garin Jos kafin ya shiga harkar fim
Sadiq Sani na da kanne guda takwas, sannan kuma a yanzu haka ya na da mata da suke zaman aure mai inganci.
.
Ku biyo mu danjin yanda akai yazama Dan jarida
0 comments: