Monday, 13 August 2018

Ku karanta fira da Fatima, sambaleliyar budurwa mai shekaru 20, diyar Jarumi Rabi'u Rikadawa



Majiyar mu ta jaridar Daily Trust ta zanta da Fatima Muammad Rabi'u, sambaleliyar budurwa mai shekaru 20 a duniya dake zaman diya ga fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Rabi'u Rikadawa wanda aka fi sani da 'Dila'.


Majiyar ta mu da ta tambayeta ko ya zata kwatanta mahaifin nata, Fatima ta cewa mutum ne mai kwazo da son yaga ya kyautatawa iyalin sa sannan kuma yana zama suyi fira cikin nishadi da annashuwa.


Da aka tambayeta me tafi so game da mahaifin nata kuma sai ta cewa ta matukar kaunar yadda yake kokarin zama tare da su duk kuwa da irin yanayin aikin sa mai cin lokaci ne da yawa.

Haka zalika Fatima ta bayyana cewa babban abun da ke batawa mahaifin ta rai shine idan har ya sanyaka abu amma kaki yi.

 Da aka tambaye ta ko ya take ji a matsayin ta na diya ga fitaccen jarumin sai ta ce takanci nauyi sosai yadda ake girmamata ana bata wata kima fiye da sauran sa'annin ta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: