Monday, 13 August 2018

Kar muke kallon ku, masu yunkurin tsige Saraki da mataimakinsa - PDP





Bayan Yar tsamar da yake faruwa tsakanin gwamnatin tarayya da majalisar kasar nan, jam'iyyar PDP ta bayyana gano wani tuggu da ake kullawa na kama shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu bayan an tsige su daga mukamansu.

Jam’iyyar PDP ta gano wani shiri da ake na kokarin kamawa tare da tsare shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu, da Jam’iyyar APC ta ke yi shirin yi.


Cikin wata sanarwa da kakakin Jam’iyyar ta PDP Kola Ologbondiyan ya fitar jiya, ya ce a cikin fadar shugaban kasa akwai wani shiri da ake kullawa na kokarin yin amfani da jami'an tsaro tare da hukumar EFCC wajen kame shugaban majalisar tare da mataimakinsa.


Sanarwar ta kara da cewa “Sabon yunkurin na kame shugaba da mataimakin majalisar dattawan yana samun goyon bayan wasu manyan jami'an fadar shugaban kasa, kuma sun himmatu wajen ganin da zarar majalisar ta dawo daga hutu za ta yi amfani da Sanatocin Jam’iyyar APC wajen tsige shuwagabannin daga kan mukaminsu".


Jam’iyyar ta PDP ta kuma kara yin zargin cewa, “Bayan an tsige shugabancin majalisar ta dattawa, akwai kuma amfani da hukumar EFCC wajen garkame Saraki da Ekweremadu tare da iyalinsu, abokansu da dukkanin wani wanda yake na kusa da su, domin duk dai a bata musu suna"


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: