Wednesday, 8 August 2018

Bincike Ya Nuna Ba A Ba Jarirai Miliyan 78 Nonon Uwa A Farkon Rayuwarsu

An kiyasta cewar, kimanin jarirai su miliyan  78 ba’a shayar dasu Nonon Uwa ba A cikin awarsu ta farkon rayuwa ba, inda hakan yake jefasu a cikin hadarin iya mutuwa da kamuwa da wasu cututtuka hakan kuma zai janyo masu kin ci gaba da shan Nonon na Uwa. 

Wannan kiyasin yana kubshe ne a cikin rahoton hadaka da Asusun tallafawa yara na duniya  UNICEF da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO suka fitar, inda suka yi nuni da cewar, lamarin yafi aukuwa a kasashe masu karamin tattalin arzkin kasa da kuma matsakaita.

Acewar rahoton, jariran da aka haifa aka kuma shayar dasu Nonon Uwa a cikin awa ta farko sunfi tsallake mutuwa. Babbar Darakta ta UNICEF, Henrietta Fore, ta sanar da cewar jinkirin da ake samu na ‘yan awowi bayan an haifi jariri ba ‘a kuma shayar dashi Nonon Uwa ba, zai iya zama barazana a lafiyarsa. Ta yi nuni da cewar hada jikin da Uwa zata yi da jaririnta a lokacin da yake shan Nono, zai sanya Nonon Uwa yafi fitowa, inda kuma jaririn zai dinga amfana da Nonon da kuma  sanadaran colostrum. 

Acewar rahoton, shayar da jarirai Nonon Uwa a cikin awa ta farko da aka haifesu, yafi yawa a Yammaci da Kudancin Afrika, inda suke da kashi  65 bisa dari amma hakan ya yi kasa a Yammacin nahiyar Asiya da kuma yankin tekun na (Pacific), inda suke da kashi  32 bisa dari. Shima a nashi tsokacin Darakta Janar na WHO Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesu yace, shayar da jariri Nonon Uwa Tana baiwa jarirai cikakkiyar lafiya a farkon fara rayuwrsu kuma ya kamata a baiwa iyaye mata goyon baya don baiwa yayknsu irin rayuwar data dace. 

Rahoton wanda ya yi fashin baki akan bayanan da aka samo daga kasashe saba’in da biyar, ya nuna cewar duk da mahimmancin da shayar da jarirai Nonon Uwa yake dashi, wasu iyayen masu shayarwa suna barin hakan ya wuce awowi a bisa wasu dalilai na kashin kansu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: