Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'ada sun yi yunkurin shigowa garin Yanware dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara a daidai lokacin sallar isha'i amma mutanen garin sun yi wa barayin turjiya ta hanyar mayar musu da harbin bindiga kuma sun kore su.
Saidai ana zaton sun harbi wasu daga cikin mutanen garin, kuma ba a tabbatar da ko mutum nawa ne ba.
Wasu mazauna yankin da wakilin RARIYA ya zanta da su, sun yi kira ga hukumar sojojin Nijeriya da su kawo musu daukin jami'an tsaro na dindindin a wannan yankin.

0 comments: