Thursday, 16 August 2018

Shekarau Ya Taimaki Addinin Allah A Jihohin Kudu

Ban taba sanin cewa tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya taimaki addinin Allah a jihohin kudu kamar haka ba.
Ance a Lokacin da yake gwamnan Kano; al’ummar musulmi mazauna jihar Enugu suna samun matsala wajen binne gawa wanda har sai sun sayi wajen da zasu binne gawa da kudade masu tsada, shine don ya saukakawa musulmi mazauna Enugu Malam Ibrahim Shekarau sai ya saya musu makeken fili suka mayar makabarta

Kasancewar sansanin matasa masu bautar Kasa (NYSC camp) a jihar Enugu dakunan kwana hade yake da na maza da mata suke cakuduwa su kwana su tashi tare babu ruwansu a hade ake daki guda maza da mata, to don a rage barna da fasadi da zinace zinace Malam Ibrahim Shekarau shi ya fitar da kudi mai yawa ya ginawa musulmi dakin kwana hotel na maza dabam da na mata a cikin NYSC camp na jihar Enugu

A jihar Imo, Owerri Ibrahim Shekarau ya gyarawa musulmi mazauna jihar babban masallacin garin saboda zubar ruwa da yakeyi, sannan ya gina musu magewayi ko bandaki guda 50 na maza da mata, bayan haka ya gina NYSC camp na musulmai a jihar Imo, ya kuma sayi makeken fili wa musulmai ya zama makabarta, kamar yadda yayi a Enugu sannan kuma ya gyara masallacin Kasuwar hausa ta Owerre.

A jihar Cross-River, Obudu, ya gina musu babban masallaci wanda da ba masallaci a garin ma gaba daya
A garin Ikoli-ogoja ya gina musu bohol a babban makarantar Islamiyyah na garin, wanda kafin ya gina musu bohol din suna anfani da gurbataccen ruwa mai warin man fetur wajen yin tsarki da alwala.
Malam Ibrahim Shekarau a wancan lokaci ya Lura da karanci wadannan abubuwa a wannan yanki ne yasa ya kai musu dauki.

Wannan abin farin ciki ne 'yan uwa musulmi, mutumin kirki mai kishin addini ne zai iya aikata haka, shiyasa naji babban malaminmu Ash-sheikh Dr Ahmad Gumi (H) yana cewa Ibrahim Shekarau yana daya daga cikin gwamnonin da suka taimaki addinin Allah suka yiwa musulunci hidima, ni dai Datti bana tare dashi a ra'ayin siyasa, amma daga yanzu idan anzo batun siyasa na dena zafafa kalmomi akanshi albarkacin taimakon musulunci da yayi, ina ma ace ya fice daga jam'iyyar PDP ya dawo tawagar Baba Buhari Maigaskiya?

Kuyi hakuri 'yan uwa da abokai, ni mutum ne wanda Allah Ya saka min so da kaunar masu taimakon addinin Allah
Muna fatan Allah Ya karawa rayuwarsa albarka Ya saka masa da alheri Ya nesanta tsakaninsa da masu bashi muguwar shawara

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: