Sunday, 19 August 2018

Fa’idoji na yin aure a maimakon zaman gwaranci a rayuwa

Masana sun bayyana cewa masu iyali sun fi gwauraye lafiya kamar yadda bincike ya nuna. Aure yana da fa’idoji da-dama ta fuskar kiwon lafiya. Wadanda su ka tsufa ba tare da aure ba ma su kan yi fama da matsaloli iri-iri.

Wanda yayi aure cikin farin ciki dai zai zauna da zuciyar sa kalau sannan kuma ba zai rika fama da masifar sha’awa ba.

Ga dai kadan daga cikin amfanin yin aure:

1. Tsawon rai

Masu iyali sun fi tsufa a Duniya kuma akwai yiwuwar maras mata ya mutu ya bar mai iyali kamar yadda bincike ya nuna. Gwauraye kan yi fama da wasu cututtuka da masu iyali ba su fama da su. Don haka sai mutum ya garzaya ya nemi aure.


2. Daukar fadi-tashi

Masu aure sun fi kokarin fama da fadi-tashi na rayuwa kuma wahalar Duniya ba ta yi masu illa kamar yadda gwauraye su ke shan wahala. Wahalhalun Duniya na jawowa mutum cututtuka irin na zuciya da ke hallaka ‘Dan Adam ana zaune kalau.

3. Fama da hawan jini

Bincike ya nuna cewa ko da wadanda su kayi gadon cutar hawan jini su kan samu sauki idan su kayi aure. Aure na kuma rage kamuwa da cutar kansa da cutar dimuwa ta tsufa da kuma ciwon sukari har da ma kansa mai kashe kwayoyin jiki.

Wadanda su kayi aure dai sun fi samun natsuwa da kamala da cika kuma har-wa-yau kwakwalwar su da zuciya ta fi zama cikin natsuwa da rashin hargitsi irin Gwauraye da Tazurai.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: