A yau Litinin, 20 ga watan Agusta ne Musulmai fiye da miliyan biyu daga sassa daban-daban na duniya ke hawan Arfa, inda za su shafe ranar suna gudanar da ibada da neman gafara ga Allah (SWT).
Wadanda suke da iko da koshin lafiyar hawa dutsen Arfa kan yi kokarin aikata hakan domin koyi ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
A filin Arfa Musulmai za su sallaci Azahar da La'asar a matsayin Kasaru, sannan a ci gaba da ibada da zikiri da karatun Al-Kur'ani tare da neman gafara daga Allah madaukakin sarki.
'Yan Najeriya sama da 55,000 ne suke aikin Hajjin bana, cikinsu har da wadannan matan da ke cikin tantunansu.
0 comments: