Ikon Allah
Ikon sai kallo, don kuwa anan wata mata mai shekaru 33, Zainab Salisu ce ta haifi yaya hudu a lokaci daya a sansanin yan gudun hijira dake garin Maradun, cikin jihar Zamfara, inji rahoton Daily Nigerian.
Malama Zainab wand ta fito daga kauyen Gidan Dan-guntu ta haifi ya hudu, biyu maza, biyu mata a ranar Lahadi, 19 ga watan Agusta, ba tare da ta gamu da wata matsala ta haihuwa ba.
Mahaifin jariran, Malam Salisu yace sau daya matarsa Zainab ta taba zuwa Asibiti don yin awo “sakamakon hare haren yan bindiga, bata iya komawa asibitin ba, don haka muke bata kulawa a gida, sai dai cikinta yayi kato sosai, amma dayake ta haihu sau bakwai a baya, kuma har yan biyu ta haifa, sai bamu damu ba.” Inji shi.
Wasu jarirai yan hudu.
Salisu bayan Zainab ta haihu, sai jami’an sansanin yan gudun hijirar suka garzaya da ita da yaran zuwa babban asibitin yariman bakura dake cikin Gusau, don samun ingantaccen kulawa.
Zainab da Mijinta na daga cikin akalla mutane dubu ashirin da suka rasa matsuguninsu sakamakon hare haren yan bindiga da yayi kamari a yankunan kananan hukumomin Maru, Maradun, Zurmi, Shinkafi da Anka, duk a jihar Zamfara.
Monday, 20 August 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: