Tuesday, 21 August 2018

Shugaba Buhari zai bude katafaren sabon kamfanin giya a jihar Ogun


Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da wani katafaren kamfanin giya mallakar International Breweries PLC (IB Plc) da aka gina kan kudi $250m, da ke rukunin kamfanoni ta Flowergate da ke tagwayen titin Sagamu-Abeokuta a jihar Ogun kamar yadda The Nation ta wallafa.


IB Plc mallakar AB InBev Group ne itace kamfanin giya mafi girma a duniya tana da ababen sha da suka hada da Eagle lager, Trophy, Hero, Betamalt da Castle lite. A kwanakin baya kamfanin da kaddamar da sabuwar giya mai suna Bedweiser.

Wannan itace matatar giya na hudu da kamfanin ta kafa a Najeriya bayan wadanda take dasu a Ilesa, Onitsha da Portharcourt wanda hakan na nuna cewa Najeriya kasa ce da ke iya janyo hankalin masu sanya jari daga kasashen waje.


A yayin da ya bayar da sanarwan ga manema labarai a harabar kamfanin a jiya Litinin, Manajan kamfanin, Mr Tony Agah ya ce wanna n kamfanin zata kasance mafi girma a Afrika bayan kamfaninsu dake Afirka ta kudu.
Agah ya kara da cewa kafa kamfanin zai samar da alkhairi sosai ga jama'an jihar Ogun da kewaye saboda ayyuka da zasu samu tare da bunkasa kasuwanci.


Acewarsa, sauran manyan bakin da su yiwa shugaba Buhari rakiya wajen taron kaddamar da kamfanin a ranar 28 ga watan Augusta sun hada Ministan Kasuwanci da Masan'antu, Mr Okechukwu Enelamah, Ministan Kasafin kudi da tsare-tsare, Mr. Udo Udoma, Shugaban Kasuwar hannun jari, Mr Oscar Onyeama da Shugban AB InBev na duniya, Mr. Carlos Britwill.

Kazalika, Manaja kamfanin, Annabelle Degroot ta ce gina kamfanin zai taimakawa Najeriya a yunkurinta na samarwa jama'a ababen sha masu nagarta da za'a rika sarrafawa a gida Najeriya.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: