Wednesday, 8 August 2018

Ikon Allah: Wata mata mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure

Wata mata ta samu karuwar haihuwa a lokacin da ta cika shekaru 60 a duniya,matar ta samu juna biyu ne a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aure
majiyar naij.com ta sanar da ita cewar matar ta samu haife diyar ta mace cikin koshin lafiya Wata mata, Grace Arowojolu, ta samu haihuwa a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aurenta. matar ta haifi diyar ta mace cikin koshin lafiya.

Naij.com ta ci karo da wannan labari ne a shafin sada zumunta na Facebook na Funmi Akeju, wata ‘yar uwa ga Arowojolu.

Dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure Akeju ta rubuta, “jama’a ku taya ni yiwa ubangiji godiyar nuna ikonsa a kan ‘yar uwa ta mai shekaru 60 a duniya da ta samu haihuwa a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aure. Daga cikin mutanen da suka tabbatar da labarin haihuwar Arowojolu akwai Ogundare Modupe Christy wacce ta kasance daya daga cikin ma’aikatan asibiti da suka karbi haihuwar dattijuwa Arowojolu.

Ajama tayi addu’ar neman karin lafiya ga mai jego da kuma diyar ta,labarin haihuwar na Arowojolu ya matukar bawa jama’a mamaki, musamman idan aka yi la’akari da yawan shekarunta na haihuwa.

Masana harkar lafiya da likitoci sun sha bayyana cewar yana da matukar wuya ga matar da ta wuce shekaru 50 a duniya ta dauki ciki balle ma ta kai ga haihuwa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: