TEEMA MAKAMASHI TA SACI WAKAR HAUWA FULLOU YAR FULANIN GOMBE (MAI WAKAR YANKARI)
Game da satar waka da ake ta cece kuce akai, akwai bukatar waiwaye game da ita wakar, mai wakar da kuma zahirin mai yake wakana da kuma mai zai biyo baya. Tunda dai wannan al’amari na satar fasaha ya riga yayi kakatu a cikin sana’a ta kirkira da fasaha a Nijeriya.
Sai kuma gashi yanzu hakan wannan dabi’a ta canza salo, inda su kansu masu wannan sana’ar ke yiwa juna satar fasaha. A cikin satin nan ne jarumar nan Fatima da aka fi sani da Teema, ko kuma Teema Makamashi (Jakadiyyar FKD) ta yi video akan wakar da aka yita da Fulatanci mai suna “General Buhari Allare Ni". Sa’annin bayan fitar da wannan waka ne, ita asalin mai wakar da aka fi sani da “Hauwa Fullou YAR FULLANIN GOMBE ta fito tayi korafin cewa wakarta ce, kuma ba tare da izininta ba ita Teema ta haikewa wannan wakar. Da yake wanann waka ta zumunci ce da aka kaddamar da ita a taron Fulani na duniya da akayi a kasar Cameroon inda sarkin yola ya kasance uba ga fulanin Nigeria, Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance Sarkin Fulanin Nigeria haka kuma gwamnan kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya zama President na fulanin Nigeria.
Wani ka iya tambayar wacece mawakiyar? Sunanta Hauwa Fullou,amma anfi saninta da Hauwa Yar Fulanin Gombe, ko kuma Mai Wakar Yankari. Mawakiya ce da aka fi sani da yin Wakoki da yaran Fulatanci, kusan ita kadai ce a duk fadin yankin yammacin Africa, tun daga Nijeriya, Kamaru, Nijar, Mali da kuma Ghana.
Ta halarci tarruka daban – daban, a inda suka yi waka tare da irinsu Umma Sangale ta kasar Mali, haka kuma ta halarci konsat a kasar Burkina Faso inda tayi waka da Dicko Fiss. A Nijar kuma sunyi waka da Yakubu Mumini haka kuma da Baba Sadu na kasar Cameroon.
Magabatan fulanin duniya sun karramata wandanda suka hada da, Abbo Ncaundere Baban Fulanin Duniya, Kadiri Yaya da kuma shi kansa President Tabbital Pulaku Na Duniya.
A yadda al’amura suke wakana, idan ba tufkar akayiwa hanci ba, satar fasaha da ta addabi Fina – Finai a Nigeria zasu mamaye harkar wakoki nan bada dadewa ba. A nata bangaren, Hauwa Fullou Yar Fulanin Gombe Mai Wakar Yankari ta tabbatar da cewa wanda yake da alhakin daukar nauyin wakar zai kai kara domin bin kadin wannan satar fasaha.
Wednesday, 15 August 2018
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: