Thursday, 9 August 2018

Musha Dariya: Tafiya Daga Kano Zuwa Lagos

An fara tafiya kenan sai tsohuwa dake cikin passengers tace Mallam Driver idan an je Kaduna ka sanar dani, driver yace to Baba.
An jima kadan Tsohuwa ta sake cewa Driver idan an zo Kaduna ka fada min fa, Driver ya hasala yace Gyatuma ai naji kuma ban manta ba, aka ci gaba da tafiya, can a wajen Kura tsohuwa ta sake nanata zancenta, yanzu kam sauran passengers ma sai da suka ji haushinta, aka ce haba gyatuma ai ko Driver ya manta zamu tuna masa Amma kin dake sai kace wanda za'a sace ki.. Wasu daga ciki suka ce ayi hakuri gigin tsufa ne !

Allah cikin ikon sa tsohuwa ta kwanta barci, Driver kuma Allah ya mantar dashi, haka ma sauran mutanen dake motar duk suka manta, tsohuwa bata farka daga barcinta ba sai da tafiya tayi nisa, tsakaninsu da Ikko bai fi 50km, sai tsohuwa ta farka, tayi mika tayi hamma tace da na har yanzu ba'a zo Kadunan bane?

Nan take kowa hankalinsa ya tashi, aka fada wa tsohuwa halin da ake ciki, nan take ta rusa kuka.. Da jama'a suka ga haka sai aka yi shawara' akan cewar dole driver yayi hakuri a koma Kaduna tunda matar nan ta tsufa da yawa, kuma bata da laifi tunda tayi ta nanatawa..

Aka yi karo-karo aka karawa driver kudin mai aka juyo Kaduna, can wajen Magriba aka iso, aka ce Baba gashi anzo Kaduna...
Tsohuwa tayi mika ta juya tace mun zo? Akace kwarai Kuwa, tace to Alhamdulillahi, tasa hannu ta bude jakarta ta hannu! Ta lalima ta dauko PANADOL dan gwangwani guda biyu, ta jefa a baki ta bishi da ruwa, tace dama Jikata ce ta bani guda hudu tace lallai lallai nasha 2 a Kaduna maganin gajiya ne, in mun isa Ikko na karasa 2, to tun da yanzu nasha na Kaduna sai kuma munje Ikko sai nasha sauran biyun.

Idan kai ne driver ko kana daya daga cikin passengers ya za kayi?

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: