Monday, 13 August 2018

Musha Dariya: ‘Yan Fulani An Shiga Birni Kallon Wasan Biri

Wasu fulani ne su uku sun shigo birni sai suka ga ana wasa da biri suka tsaya suna kallo akace biri yayi tafiyar karuwa ta ga mai kudi Biri yai far da ido yana tafiya yana yanga da kwarkwasa kai ka ce wata tsohuwar karuwa a kai ta sanya shi yana kwaikwayon abubuwa daban daban yana yi aka ce yayi tsallen kwado sai ya yi.


Sai Dan fulani yaji haushin biri ya ce yau ga shege.

Sai aka ce biri yi zaman Dan fulani shanu sun kare sai biri ya dauko sandâ ya sa a kafadar shi ya lankwashe kafarsa ya murtuke fuska ya zare ido ya langabe kai jikin sanda.

Dan fulani na ganin haka ya bushe da dariya ha ha ha ha ha ya ce “Kwal uba Aradu kamar Baffa nah!!!”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: