Sunday, 19 August 2018

Rikita-rikitar Da Kan Iya Kunno Kai A Cikin Jam'iyar PDP Bayan Zaben Fidda Gwani

Yawaitar masu neman takarar Shugaban kasa a jam'iyar PDP kan iya zamewa jam'iyar matsala bisa la'akari da yadda wadanda suka sake dawowa cikin jam'iyar ke kokarin mamaye dukkan harkokin jam'iyar tare da maida wadanda suka himdimtawa jam'iyar saniyar ware.
Rikicin kan iya barkowa a lokacin da jam'iyar tayi zaben fidda dantakarar Shugaban kasa, kuma dantakarar ya fito a bangaren wadanda suka dawo cikin jam'iyar a baya bayannan.

Wata majiya mai tushe ta habarto wani mai neman jam'iyar PDP ta tsaida shi takara yana cewar, muddin jam'iyar ta bada takara ga mutanen da suka gujeta abaya, to ko shakka babu zasu nade hannu su zauna subar jam'iyar da iyawarta.

A wani kaulin kuma, wani dantakarar ya koka da cewar tundawowar masu sauyin sheka daga jam'iyar APC zuwa PDP, jam'iyar PDP ta fara baya baya dasu duk da cewar abaya jam'iyar tana gudana ne da aljifan su. Sannan yasha alwashin cewar muddin jam'iyar ta hanashi takara, ko shakka babu bazai sake bata tallafin gudanarwa ba.

A bangare guda kuma dukkan wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyar PDP, sun sauya shekar ne da zummar samun tikitin tsayawa takara a zaben 2019, yayinda wasu ke neman jam'iyar ta tsaidasu takarar Shugaban kasa, wasu kuma majalisun dokoki suke bukatar jam'iyar ta tsaidasu. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akwai wadanda suka jima suna yiwa jam'iyar hidima tare da biyayya domin jam'iyar ta tsaida su takarar wadannan kujeru, muddin jam'iyar ta hanasu takarar ta fifita wadanda suka sauya sheka akansu, to fa suma wata hanyar zasu nema wacce zata bulle masu.

Ire-iren wannan koke koken yasa masu fashin baki akan harkokin siyasa ke ganin jam'iyar PDP kan iya samun matsala bayan gudanar da zaben fidda dantakara.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: