Sunday, 19 August 2018

Obasanjo Ba Zai Hana 'Yan Nijeriya Sake Zaben Buhari Ba, Inji Tinubu

"Shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari ya taka rawar gani, don haka ya cancanci mulki a zango na biyu, kuma za mu mara masa baya domin yin nasara saboda mutuminmu ne.
"Ku manta da wasika Obasanjo da kuma yawan kalubalantar Buhari da yake yi saboda ba zai hana 'yan Nijeriya sake zabensa ba.

"Obasanjo ya yi nasa lokacin, don haka ya rabu da Buhari ya fuskanci harkokin gabansa, domin ba zai gaya mana wanda za mu zaba ba.

"Obasanjo yana daga cikin matsalolin da muke fuskanta a kasar nan a yau, saboda bai dora kasar kan turba nagari ba a lokacin da yake shugaban kasa", inji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: