Ya zama dole majalisa ta dawo zama ba tare da bata lokaci ba – APC
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi kira ga majalisar dokokin kasar da su dawo zama a tare da bata lokaci ba.
Jam’iyyar tayi wannan kira ne a ranar Juma’a a wata sanarwa daga mukaddashin sakataren labaranta, Mista Yekini Nabena.
Ta bukaci bangaren dokoki da suyi gaggawar kula da muhimmancin kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta domin zaben shekara mai zuwa.
Jam’iyyar APC tace hukumar zaben kasar na fuskantar barazana ta hanyar zargin cewa ana shirya manakisa domin a aga gazawar hukumar INEC a zaben 2019.
Ta kuma zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da shugaban majalisar dattawa da yunkurin fakewa da dokar gyaran zabe domin janye hankalin jama’a daga dawowa majalisa.
APC tayi kira ga Yan Najeriya da suyi Magana sannan su tabbatar da cewa majalisar dokokin kasar ta aiwatar da ayyukanta daidai da tsarin da kundin tsarin mulki ta tanadar.
0 comments: